Yadda Ministar jin Kai tayi auren sirri da shugaban sojin saman Najeriya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, September 25, 2020

Yadda Ministar jin Kai tayi auren sirri da shugaban sojin saman Najeriya


 Yadda Ministar jin Kai tayi auren sirri da shugaban sojin saman Najeriya


Tun bayan da labarin ya fara yaÉ—uwa kan batun auren Ministar Jin-Æ™ai da kare Afkuwar Bala'i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq da shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Sadiq Abubakar, mutane da dama suka fara neman sanin gaskiyar labarin.


Binciken da BBC tayi ta hanyar tuntuɓar wasu makusantan ma'auratan biyu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru, kuma an ɗaura auren ne tun a Juma'ar makon da ya gabata.


Majiyoyin masu ƙarfi ta ɓangaren Minista Sadiya da Air Marshal Sadiq da suka buƙaci a ɓoye sunayensu sun ce an ɗaura auren ne cikin sirri a Abuja babban birnin Najeriya.


Sai dai daga Ministar har shugaban rundunar sojin saman ba su fito sun gaskata ko ƙaryata batun ba har yanzu.


Sai dai Æ´an Najeriya da dama na mamakin yadda za a É—aura auren fitattun mutane irin waÉ—annan amma ba a bayyana lamarin ba, musamman ganin cewa aure abin alkhairi ne ba abin É“oyewa ba.


Amma É—aya daga cikin majiyoyin ya ce, ''ai babu inda aka ce dole sai mutum ya bayyana aurensa, idan dai an cika sharuÉ—É—an auren yadda ya kamata bisa tsarin Musulunci ai shi kenan an samu abin da ake so.''


Wata majiyar kuma ta daban cewa tayi ''ba a bayyana auren bane saboda yanayin da ake ciki na ƙoƙarin taƙaita yaɗuwar cutar korona da bin ƙa'idon da gwamnati ta gindaya.''


A bara ne Najeriya ta É—auki É—umi bayan da wani labari ya yaÉ—u kamar wutar daji da ke cewa ministar ta auri Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai daga baya ya bayyana cewa labarin ƙarya ne.


An yi ta yaÉ—a wasu hotana da ma'auratan biyu da suka É—auka tare, yayin wata ziyara da Air Marshal Saidq ya kai ofishinta, wanda Hajiya Sadiya ta wallafa a shafinta na Tuwita tun a watan Maris, ana tattauna batun auren da su.


Sai dai hakan bai isa hujja ta cewa ko a lokacin suna tare a matsayin masoyan juna ba.


Amma binciken da BBC tayi daga waÉ—annan makunsantan ma'auratan ya tabbatar da cewa 'sun É—an jima tare, sai dai auren ne Allah bai kawo lokacinsa ba sai yanzu,'' a cewarsu.


Kafar yaɗa labarai ta PR Nigeria ma a nata rahoton ta tabbatar da cewa ta tattauna da wani malamin addinin Musulunci da ya shaida ɗaurin auren, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, inda yace ''shi aure a Musulunce ba dole sai ma'auratan sun halarci taron ɗaura shi ba, waliyyansu kaɗai sun wadatar".


''Ɗaurin auren ya samu halartar shaidu da kuma waliyyan ango da na amarya, da biyan sadaki da karatun Al-ƙur'ani. Kuma waɗannan su ne abin da aka fi so a samu a wajen ɗaura aure,'' a cewar malamin.


Ƴan Najeriya da dama sun yi tayi wa Hajiya Sadiya da Air Marshal Sadiq fatan alheri kan wannan aure nasu musamman a shafukan sada zumunta.


Da yawa addu'o'in zaman lafiya da samun zuri'a ta gari suka dinga yi musu.


Takaitaccen tarihin Sadiya Umar Farouq

Sadiya Farouq ta kasance wacce aka fi yawan magana a kanta cikin ministocin Buhari.


Kafin ba ta mukamin Ministar Kula da Ayyukan Jinkai da Kare Afkuwar Bala'i da Ci-gaban Al'umma, Sadiya Farouk ce shugabar Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci rani da wadanda rikici ya raba da muhallansu.


Don haka, ana iya cewa ta dade tana aiki da masu karamin karfi da gajiyayyu.


Sadiya Umar Farouk ta taba yin Jami'ar Kula da Asusun Jam'iyyar APC ta kasa daga watan Yunin 2013 zuwa watan Yunin 2014.


Daga nan ne kuma ta zama mamba ta majalisar kamfe din shugaban kasa a jam'iyyar ta APC, inda ta rike mukamin shugabar kwamitin tsarawa da sa ido da kaiwa-da komowa da samar da kudi.


Sadiya Farouk ta jagoranci tawagar da ta shirya zaben 2015 a jam'iyyar APC wadda kuma tayi nasara.


Tsakanin shekarar 2011 da 2013, Sadiya Farouk ta rike mukamin Mai Kula da Asusun Jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), jam'iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2011


Jam'iyyar CPC na daya daga cikin jam'iyyu hudu a Najeriya da suka hadu suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2013.


Sadiya Umar Farouk 'yar asalin karamar hukumar Zurmi ce a jihar Zamfara kuma tana da digirin farko a bangaren Kasuwanci sannan digirinta na biyu a bangaren Diflomasiyya.


Ita ce mafi karancin shekaru a ministocin Shugaba Muhammadu Buhari inda take da shekara 45 da haihuwa.


No comments:

Post a Comment