An kashe ɗan sanda da 'yan Boko Haram shida a Yobe - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, October 25, 2020

An kashe ɗan sanda da 'yan Boko Haram shida a Yobe


  An kashe ɗan sanda da 'yan Boko Haram shida a Yobe

Wani ɗan sanda da kuma mayaƙan ƙungiyar Boko haram shida sun rasa rayukansu yayin wata fafatawa a Jihar Yobe.


Kakakin "Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa da Kafar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin a jiya Asabar.


Lamarin ya faru ne a Babban Gida biyo bayan harin da 'yan bindigar suka kai a cikin motoci ƙirar Toyota Hilux guda huɗu da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Asabar.


Garin Babban Gida yana da nisan kilomita 50 daga Damaturu, babban birnin jihar.


Wakilin kafar talabijin na Channels ya ga dakarun sojan Najeriya na yunƙurin fita domin tunkarar maharan.


Kazalika, rahotanni sun ce an cinna wa wasu ɓangarori na ofishin 'yan sandan yankin wuta da kuma wani sansanin sojoji.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

No comments:

Post a Comment