Ga wasu daga cikin muhimman batutuwa shida da ya yi tsokaci a kansu, yayin jawabin na sa.
1. Damar zanga-zanga
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince kan cewa ba shakka al'ummar kasar na da damar yin zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya basu dama, sai dai sashen ya buƙaci a kiyaye doka a kuma kauce wa shiga hakkin jama'a.
Ya ce su kansu matasan da suka fito suna zanga-zangar EndSARS da farko sun yi tane cikin lumana, kafin daga bisani wasu ɓata gari suka fake da ita wajen haifar da yamutsi da tayar da hankalin jama'a, da kuma ƙona gine gine da ƙadarorin gwamnati.
Ya bayar da misalin fadar mai martaba Oba na Legas da É“ata gari suka kai wa hari, da kuma kutsa wa filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke Legas da suka yi.
2. Ba za mu amince da tayar da zaune tsaye ba
To sa dai a cewar Shugaba Muhammadu Buhari, duk da sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa 'yan kasa damar yin zanga-zanga, ya kuma yi gargaÉ—i a kan tayar da yamutsi da sunan Zanga-zanga.
''Babu ta yadda za mu amince da tayar da zaune tsaye, mun ji kokenku yadda ya kamata, muna kuma É—aukar matakai a kansu.
Shugaban ya kuma yi kira ga 'yan kasar su koma harkokinsu, bisa alkawarin cewa jami'an tsaro za su cigaba da ƙoƙarin kare lafiya da dukiyoyinsu musamman 'yan sanda.
3. Walwalar Æ´an sanda
Dangane da walwalar 'yan sanda, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai don tabbatar da walwalarsu, ta yadda za su kiyaye rayukan jama'a yadda ya kamata.
''Mun bai wa hukumar kula da albashi umarnin sake nazartar albashin 'yan sanda, har ma da sauran hukumomin da suka hadar da na hukumar kashe gobara.
Gwamnati za ta cigaba da kare rayuka da dukiyoyin jama'a, ta yadda za su koma harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.
4. Yaƙi da talauci
Shugaban ya bayyana cewa babu wata gwamnati a Najeriya da ta ɗauki gabarar yaƙi da talauci ta hanyar bijiro da matakai daban-daban na magance su kamar tasa, don haka ya kamata masu zanga-zangar su lura cewa da gaske yake wajen shawo kan matsalolin da suka shafi matasan Najeriya.
Ya lissafo wasu shirye-shirye da gwamnatinsa ta bijiro da su da tuni suka fara aiki domin rage talauci a tsakanin 'yan Najeriya.
Wasu daga cikinsu da ya lissafo sun haÉ—ar da :-
Farmermoni,
Tradermoni,
Marketmoni,
N-Power,
N-Tech and
N-Agro.
5. Takaicin rasa rayuka da gargaÉ—i kan yaÉ—a karya game da gwamnati
''An yi ta'adi sosai duk da sunan zanga-zangar EndSars. Na ji matuƙar taƙaici kan irin asarar rayuka da dukiyoyi da akayi. Waɗannan masifun ba su dace ba. Bai kamata a aikata irin waɗannan abubuwa da sunan bayyana takaicin da matasan ƙsarmu ke ciki ba.
''Sannan irin yadda ake yaɗa labaran ƙarya a shafukan sada zumunta da sunan cewa wannan gwamnatin nan bata damu da halin da ƴan ƙasarta ke ciki ba, tuggu ne na son karkatar da hankalin mutane a ciki da wajen ƙasar wajen yi wa gwamnatin rashin adalci,'' in ji shugaban.
6. Martani ga kasashen duniya
Shugaban bai gushe ba, sai da yayi magana dangane da kasashen duniya da sukayi Allah wadai dangane da bude wa masu zanga-zanga wuta da sojoji suka yi, inda yace kamata yayi su nemi ƙarin bayani ko kuma neman ainihin hujjar abin da ya faru, maimakon dogara da ɓangare guda.
''Muna gode wa dukkanin wadanda suka bayyana damuwa dangane da wannan batu, muna kuma ɗaukar matakai a kansu, amma yana da kyau a rika tuntuɓa kafin ɗaukar matsaya,'' in ji Buhari.
No comments:
Post a Comment