DALILAN DA YASA RUNDINAR SOJIN NIGERIA TA MAMAYE OFISHIN JARIDAR DAILY TRUST
Rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwa ta bakin Kakakin rundinar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka game da mamayar ofishin jaridar Daily Trust a Abuja da kuma reshen gidan jaridar da yake Maiduguri Jihar Borno
Rundinar sojin Nigeria tace tana sanar da al'umma cewa jami'an rundinar sojin Nigeria tare da hadin gwiwar rundinar 'yan sandan Nigeria da sauran hukumomin tsaro tabbas sunje ofishin jaridar Daily Trust dake Abuja da Maiduguri domin su gayyaci ma'aikatan gidan jaridar, a kan wani labari da jaridar ta wallafa a ranar lahadi da ya gabata, inda ta fallasa wani boyayyen shiri da rundinar sojin Nigeria keyi don ta murkushe kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram
Labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa akan shirin da rundinar soji takeyi akan Boko Haram karya alkawari ne, kuma makarkashiya ne ga tabbatar da tsaron Nigeria, sannan cin amanar tabbatar da tsaron 'kasa ne wanda ya sa6a da kundin dokar Sirri na 'Kasa (Official Secrets Act) sashi na 1 da na 2, abinda jaridar ta aikata zaisa Boko Haram su farga da shirin da rundinar sojin takeyi, kuma kamar tana taimakawa 'yan ta'addan ne domin su farga su dauki matakin kariya game da shirin da rundinar soji keyi a kansu wanda hakan zai iya cutar da su kansu mayakan sojin
Don haka rundinar sojin Nigeria tana tabbatar da cewa da saninta ta kai mamaya ofishin jaridar Daily Trust ta kuma gayyaci wadanda suke da alhakkin fallasa labarin shirin da rundinar takeyi akan 'yan ta'adda, domin su fahimci laifin da suka aikata na cin amanar tsaron Nigeria
Rundinar sojin Nigeria tana bada shawara ga gidajen jaridu masu zaman kansu da suyi kokarin bin doka da ka'ida na aikin jarida, rundinar soji bata da buri na cutar da kowace kafar yada labarai ko take hakkin aikin jarida bisa doka, amma ana shawartarsu da su guji fitar da bayanai akan shirin da rundinar takeyi wajen inganta tsaron Nigeria, rundinar soji ba zata taba kyale duk wanda ya fallasa sirrin shirin da takeyi akan 'yan ta'adda ba, domin hakan cin amanar tsaron 'kasa ne
Kuma rundinar sojin Nigeria tana kira ga dukkan kafofin watsa labarai na Nigeria da su taimakawa rundinar wajen kawo karshen kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram, rundinar sojin Nigeria tana tabbatar da cewa gayyatar ma'aikatan jaridar Daily Trust da tayi yana da nasaba da gudanar da bincike, duk wanda ta samu da hannu wajen fallasar asirin boyayyen shirinta akan Boko Haram da aka wallafa a jaridar ta Daily Trust zata mikashi ga hukumar 'yan sanda domin a gurfanar dashi a gaban kuliya
Rundinar sojin Nigeria tana kira ga jama'a da su yada wannan sanarwa da ya fito daga kakakin rundinar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka
Muna rokon Allah Ya taimaki rundinar sojin Nigeria da sauran hukumomin tsaro akan 'yan ta'adda da wadanda suke cin amanar tsaron Nigeria ta kowace hanya Amin
Daga Datti Assalafiy
Tuesday, January 8, 2019
New
DALILAN DA YASA RUNDINAR SOJIN NIGERIA TA MAMAYE OFISHIN JARIDAR DAILY TRUST
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
GIST
Tags
GIST
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment