*Menene Template*
Template shine Theme da kuke gani a Wajen Sanya Theme na blogger dinku
Sannan dole template na blogger karshensa ya kasance da Format na .xml
Dan haka akwai shafukan da suke bada free template, to amma a format na .zip suke badashi, To dole kafin kasanya shi, kayi extract dinsa ya koma .xml
Abinda ake magana anan shine file extension, wato wannan alama dake karshen kowanne irin file
Akwai mai .jar akwai .xml da sauran su
Da farko zakaje google ka searchin *Free blog templates* zasu baka sai ka downloading
Bayan ka dauko shi, zaka nemi file explorer ko *RAR* dukkansu aikinsu daya ne
Zanyi bayani yadda za'aym extracting file amma da *RAR*
bayan ka dauko shi a play store ko 9apps sai ka bude shi, bayan ka bude shi
ta hannun hagu a sama, akwai alamar menu, anan zaka shiga ka zabi storage da downloaded template din ke ciki
Zamu samu shi template din a cikin download folder, wato zamu shiga download folder kenan, bayan mun bude download folder zai nuna mana abubuwanda ke ciki
Daga nan zakaga zip file daka downloading na template din, Zaka clicking ta hannun daman nan ne, wato wannan box din, Bayan ka clicking akwai wani arrow acan sama ta gefen dama,
Wannan yake hagun alamar delete, sai ka danna shi, bayan ka danna shi zai nuno maka wasu wurare.
Idan dama akwai inda ka tanada domin ajiye su wato folder, zaka dannan browse dake sama zai nuno maka folders sai ka zabi wanda kakeso
Idan kuma bazaka canza mishi location ba, wato zaka barshi a fili kawai sai ka danna ok dake kasa
kana danna ok zai nuna maka yana loading, yana kammala zai tsaya, wato ya gama.
Zai creating maka files kamar 2, extension dinsu daban-daban.
Wanda kake buqata shine mai extension .xml wato wanda ya kare da hakan.
Zaka ga hakan ne bayan ka sauka a *RAR* dinka, ya shiga file manager, idan kayi folder zaka same shi cikin folder din, idan kuma baka mishi folder ba to yana waje, anan zaka ganshi
To yanzu mun downloading template mun extracting saura daura shi akan Blog
Idan ka shiga ta blog dinka wato blogger. com sannan ka shiga theme, a saman theme ta hannun dama gana daya, zaka ga *backup/restore* nan zaka shiga.
Bayan ka shiga zai nuna maka alamar wurin sanya file, sai ka danna, kana dannawa zai nuna maka cewa ka zabi location inda file dinka yake, sai kaje
Kana danna kan file din zan fito maka, akwai upload a kasan wurin sai ka dannan.
To idan template da ka downloading mai kyau ne zai uploading, idan mara kyau ne zai maka wani turanci cewa "some files are missing" kenan zaka sake komawa ka dauko wani ka sake extracting, idan kuma ya uploading shikenan
Yana kammalawa zai fidda ka a wurin dakanshi, zakaga theme dinka a kasa yadda yake nuna default theme.
Idan zaka customizing sai kayi, idan ka iya HTML sai kayi editing, idan baka iya su ba sai ka barsu kawai.
Sai ka hau site dinka kaga yadda theme din yake ko akwai kyau ko babu
Idan yayi maka, Masha Allah, idan baiyi ba sai kaje ka sake steps da na bada a sama.
No comments:
Post a Comment