YADDA ZA'A WARWARE SIHIRI--WANDA YA KASA KUSANTAR MATAR SA SABODA SIHIRI - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, January 31, 2019

YADDA ZA'A WARWARE SIHIRI--WANDA YA KASA KUSANTAR MATAR SA SABODA SIHIRI

YADDA ZA'A WARWARE SIHIRI--WANDA YA KASA KUSANTAR MATAR SA SABODA SIHIRI

A Tafsirin sa na ranar Juma'a 22-1-16 da yake gabatarwa a Masallacin Usman bn Affan dake gadon kaya, Dr Sani R/Lemo ya kawo bayanai da Ibn Baddal ya fada a Sharhin Bukhari kamar yadda ya ruwaito daga Wahb Ibn Munabbih.
.
Ibn Munabbih yace "Idan mutum yana son ya warware sihiri, ga yadda zai yi --sannan kuma yace wannan yana da matuqar amfani ga wanda aka masa sihiri ya kasa kusantar matarsa--sai a samu ganyen magarya kore (guda 7) sai a daka shi, sannan a zuba a ruwa, sai a karanta Kulhuwallahu da Falaki da Nasi da Ayatul Kursiyyu a tofa a ruwan, sai mutum ya sha sau 3 kuma ya yi wanka da shi, idan mutum ya yi haka to IN SHA ALLAHU Allah Zai tafiyar masa da duk abinda ke damunsa na Sihiri".
.
Shi Ibn Munabbih asalinsa Bayahude ne ya Musulunta, yana daga cikin Tabi'ai, kuma daman kafin Musuluntar sa mutum ne mai Ilimi.
.
Wannar maganar tasa wasu Malamai da yawa suna kawo ta a littattafan su, kamar Ibn Qayyim ya kawota a Zaadul Ma'ad, Ibn Kathir ya kawota a Tafsirin sa, Ibn Baddal ya kawota a sharhin Bukhari.
.
Amma sai Mallam (Dr Sani) yace "Amma wannan gwaji ne, ba wai Hadisi ne daga Manzon Allah (s.a.w) ba, don haka idan mutum ya gwada aka dace shikenan".
.
Kuma daman wasu Hausawan sunce asalin karmar "Magani" ai ana nufin  "Maa gani" ne, ma'ana za mu gwada mu gani.
.
Allah Ya sa mu dace.

No comments:

Post a Comment