Mayaƙan da ake zargi na Boko Haram ne sun auka wa garin Monguno da ke ƙarƙashin kulawar sojoji a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Ganau sun ce an kashe aƙalla mutum shida -- ciki har da sojoji da fararen hula.
Wasu rahotanni na cewa adadin waÉ—anda aka kashe yayin artabu sakamakon wannan hari na ranar Asabar ya fi haka.
An ba da rahoto cewa masu iƙirarin jihadin sun far wa garin Monguno ne da tsakar rana, inda suka riƙa harba bindigogi da rokoki, lamarin da ya sa har suka fi ƙarfin dakarun gwamnati.
Gyauron ƙungiyar Boko Haram da ake kira da ISWAP ya ce mayaƙansa ne suka kai harin, wanda yazo kwana uku bayan wani makamancinsa kan garin Gubio da yayi sanadin mutuwar kimanin mutum tamanin da daya.
Wani mutumin yankin, amma mazaunin birnin Maiduguri ya shaida wa BBC cewa mayaƙan sun rabu gida biyu ne, inda kashi na farko yayi yunƙura kutsa kai ta ɓangaren hanyar Maiduguri.
"Rahotannin da muka samu sun nuna cewa waɗanda suka yi yunƙurin shiga Monguno ta hanyar Marte, ba suyi nasara ba," in ji shi.
Ya ce an yi ta musayar wuta tsakanin sojoji da maharan, kafin a kira jiragen yaƙi, waɗanda suka riƙa shawagi tare da far wa masu tayar da ƙayar-bayan.
Ya kuma ce: "Mazaunan garin ala dole suka tsere zuwa gidajensu saboda amon bindigogi da ƙarar fashe-fashe, daga bisani ne kuma maharan suka je caji ofishin 'yan sanda, inda har suka kuɓutar da wasu dake tsare.
A cewarsa, mayaƙan sun shafe tsawon sa'a ɗaya da rabi suna ɗauki-ba-daɗi da sojoji, kafin ƙura ta lafa.
Fiye da mutum dubu É—ari na mazauna garin, rikicin Boko Haram na shekara goma ya tilasta musu tserewa daga muhallansu.
Sai dai wata majiya ta kuma ce dakarun Najeriya sun katse hanzarin maharan waɗanda suka yi yunƙurin mamaye Monguno, mahaifar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Mohammed Monguno.
Jaridar PRNigeria ta ambato wata majiyar soja a arewa maso gabashin ƙasar na cewa mayaƙan na Boko Haram sun auka wa Monguno ne da rana tsaka suna harbe-harbe a yunƙurinsu na ƙwace garin.
Sai dai haƙonsu bai cim ma ruwa ba, don kuwa dakarun sojin Najeriya sun fatattake su bayan sun samu ɗaukin jiragen yaƙi.
Majiyar ta ce yayin da dakarun ƙasa daga sansanonin sojin Monguno ke fafatawa da 'yan ta-da-ƙayar-bayan, jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya lalata motocin 'yan Boko Haram takwas da ke tserewa.
No comments:
Post a Comment