Wasu Daga Cikin Dalilan da Suka sa kuɗaɗen Cryptocurrencies Suka faɗi warwas
Farashin kuɗin intanet na Bitcoin ya yi faɗi da dala 34,000 a karon farko cikin wata uku bayan China ta sanya dokokin haramci kan masu amfani da kuɗaɗen intanet ɗin wato cryptocurrency.
A jiya Talata ne China ta hana cibiyoyin kuɗi da kamfanoni yin mu'amala da masu hada-hada da kuɗin intanet.
Haka nan ta gargaɗi masu zuba jari game da mu'amala da su a ɓoye.
Wannan ya biyo bayan faɗuwar da kuɗin ya yi a makon da ya gabata da kashi 10 cikin 100 bayan kamfanin ƙera motoci na Tesla ya ce ya daina karɓar kuɗin na Bitcoin.
Zuwa ranar Litinin, darajar kuɗin ta faɗi da kashi 22 cikin 100, faɗuwar da ta kai kusan dala 6,000 a cikin awa 24.
War On Rug da Lark Devis sun Taso Safemoon a gaba
An Taso Kamfanin Binance a gaba a Bincike akansa
A gefe guda kuma, kuɗaɗen Ethereum da Dogecoin sun yi faɗuwar kashi 25 da 29 cikin 100 kowannensu.
Ina Siyar da CLASSIC COIN da Data ta kowane Network, Mai bukata yamin magana ta WhatsApp 08122225296
No comments:
Post a Comment