An garzaya da shugaban Amurka zuwa asibitin Sojoji - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, October 2, 2020

An garzaya da shugaban Amurka zuwa asibitin Sojoji

 


An garzaya da shugaban Amurka zuwa asibitin ne bayan ya kamu da cutar korona


An tafi da Shugaba Donald Trump asibitin sojoji na Walter Reed bayan gwajin da aka yi masa ya nuna ya kamu da cutar Covid 19 wato Coronavirus.

Asibitin sojojin yana wajen birnin Washington.


Idan za a iya tunawa Trump da mai dakinsa Melania sun kamu da korona a ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba bayan wata hadimar shugaban, Hope Wicks ta kamu da cutar.


Kafin garzayawa da shi asibitin sojojin, an bawa shugaban na Amurka wasu magunguna.


Wannan bayanin na kunshe cikin wata sanarwa da likitan shugaban kasar ya fitar kamar yadda CNN ta ruwaito.


Domin siyan DATA Ta MTN 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp 08122225296


"A halin yanzu Shugaban kasar yana cikin yanayi mai kyau amma akwai gajiya tattare dashi. 


Wata tawagar kwararru na duba shi kuma tare da su zamu bada shawarar abinda ya dace a masa shi da mai dakinsa," a cewar likitan.


Shugabanin kasashen duniya da dama sun jajantawa Trump tare da masa fatan samun sauki da shi da mai dakinsa, ciki har da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.


Rashin lafiyar ta shugaba Donald Trump na zuwa ne a lokacin da kasar ta Amurka ke shirye-shiryen yin babban zaben ta a watan Nuwamba.


Hotunan yadda akayi Bikin cika Shekaru 60 da Samun Yan cin Kan Najeriya

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/hutunan-yadda-akayi-bikin-cika-shekaru.html

No comments:

Post a Comment