Muhimman jawaban Buhari na cikar Najeriya Shekaru shittin da Samun yancin Kai - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, October 1, 2020

Muhimman jawaban Buhari na cikar Najeriya Shekaru shittin da Samun yancin Kai

 


A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2020 ne Najeriya ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.


A safiyar Alhamis ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi jawabai na musamman ga 'yan ƙasar inda jawaban yafi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasar.


Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya taɓo a jawabinsa:


HaÉ—in kai

Jigo ko kuma babban saƙo a cikin jawaban shugaban ƙasa shi ne kan batun haɗin kai, domin shugaban a wurare daban-daban ya nuna cewa idan 'yan ƙasar suka haɗa kansu za a samu ci gaba mai ɗorewa.


"Idan muka haɗa kanmu za mu iya sauya yadda muke a yanzu domin kawo ci gaba mai amfani a garemu kuma za mu iya taimakon kanmu ƙwarai".


Shugaba Buhari ya bayyana cewa ta hanyar haɗin kai ne 'yan Najeriya za su magance ƙalubale daban-daban da suke fuskanta.


Tarihin Najeriya na tsawon Shekara 60 da Samun yancin Kai

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/tarihin-najeriya-na-tsawon-shekara-60.html


Warkar da Najeriya daga raunin da ta samu

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wannan wata dama ce da 'yan Najeriya za su gyara ƙasar su. A cewarsa, ya kamata mutane su kawo ƙarshen irin tunanin da suke da shi wanda bai ciyar da ƙasar gaba.


Ya ce bai kamata 'yan ƙasar na nuna wariya irin ta ƙabilanci ba, ta yadda ake nuna cewa wani ya fito daga wani yanki na daban.


Ya ce ya kamata 'yan ƙasar, su rinƙa ɗaukar kansu a matsayin ɗaya.


Ya ce domin fara warkar da irin wannan raunin, ya kamata 'yan ƙasar su fara kallon kansu a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya


Tattalin arziƙi

A jawabin sa, ya bayyana cewa yana sane da cewa tattalin arziƙin Najeriya na cikin wani hali kamar yadda na sauran ƙasashen duniya yake.


Ya bayyana cewa ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar wajen cimma burinta na zama ɗaya daga cikin ƙasashe 20 mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya.


Shugaban ya kuma sake jadda aniyarsa ta cire 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10.


El Rufa'i ya soke zaɓen farko na masu zaɓen sabon sarkin Zazzau

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/yunurin-farko-na-naa-sabon-sarkin.html


Harkar zaɓe

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya ce hali irin na ɗan adam ne ke kawo akasarin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zaɓe sakamakon yadda mutane ke son samun mulki ta kowane hali.


Shugaban ya jaddada aniyarsa ta samar da zaɓen gaskiya da adalci inda kuma ya bayar da misali da zaɓen jihar Edo da aka kammala a watan jiya.


Ya ce ya kamata zaɓen Edo ya ba 'yan ƙasar ƙwarin gwiwar cewa a shirye yake ya samar da hanyoyi da yanayin tabbatar da ƙuri'ar kowane ɗan Najeriya batayi ciwon kai ba.


Man fetur

A jawabin Shugaban, ya ce ba abin da hankali zai ɗauka bane a ce Najeriya na sayar da man fetir a farashi ƙasa da abin da ake sayarwa a ƙasashen makwafta.


Shugaban ya ce dole ne a sauya farashin man fetir. Ya ce a yanzu ana sayar da kowace lita ɗaya 161, kuma ya bayar da misali da yadda sauran ƙasashe suke sayarwa kamar haka:


Chadi na sayar da kowace lita naira 362 a kowace lita


Jamhuriyyar Nijar kuma na sayarwa kan naira 346 kan kowace lita


Ghana na sayar da kowace lita kan naira 326


Sai kuma Masar na sayar da kowace lita kan naira 211 sai kuma Saudiyya 168.


Ana fara cike neman tallafin da Gwamnatin Nigeria zata bayar na naira bilyan 75 

No comments:

Post a Comment