Ganduje ya kaddamar da kwamitin bada shawara akan harkar Community Policing da Kuma kwamaitin Community Police na bangaren jami'an tsaro - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, May 30, 2020

Ganduje ya kaddamar da kwamitin bada shawara akan harkar Community Policing da Kuma kwamaitin Community Police na bangaren jami'an tsaro

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da babban kwamitin bada shawara akan harkar Community Policing karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma kwamaitin Community Police na bangaren jami'an tsaro karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan Yan sanda na jiha wato Balarabe Sule. 

Wadannan kwamitoci saban tsari ne na gwamnatin taraiya karkashin jagorancin Inspector General na yan sanda wanda Gwamna ya kaddamar dana jihar Kano, kuma kowanne Committee na da membobi daga sassa daban daban na al'ummar jihar Kano, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano.

Sauran manyan baki sun hada da Mataimakin Gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji wanda shi ma dan kwamitin ne, da shugaban jamiyar APC na Jiha Alhaji Abdullahi Abbas
da manyan jamian tsaro daga sassa daban daban da saura masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.

No comments:

Post a Comment