Za a koma biyan Kashi hamsin %50 na albashin Masu rike da mukaman siyasa a kano - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, May 18, 2020

Za a koma biyan Kashi hamsin %50 na albashin Masu rike da mukaman siyasa a kano

Za a koma biyan Kashi hamsin %50 na albashin Masu rike da mukaman siyasa a kano


 Sakataran yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya ce wannan  ya shafi gwamnan da mataimakinsa wato Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, duk kwamishinoni, da masu ba da shawara na musamman, da manyan mataimaka na musamman, da shugabannin kana Nan hukumomi, da kinsiloli da masu taimaka musu da sakatarorin kana nan hukumomi da sauransu.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a ranar Lahadi ta hannun Babban Sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, ya ce matakin ya samo asali ne sakamakon karancin abinda ake Samu daga asusun tarayya bisa faduwar farashin man fetur da kuma rashin samun kudaden da ake samu a cikin gida, watau IGR, wanda cutar COVID-19 ta haifar.

Sanarwar ta ce: “Har ila yau, akwai koma baya a cikin tsarin tattalin arziki, saboda kalubalen cutar COVID-19. G

Ganin cewa kusan dukkanin kamfanoni a jihar basa aiki saboda kulle jahar sanadiyar Corona.

“Hakanan sauran wuraren da jihar ke samun kudaden shiga, ba su fara aiki ba. Wannan ma wani dalili ne na ba wa masu rike da mukaman siyasa rabin albashi

No comments:

Post a Comment