Kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona ya sanar da cewa an tsawaita dokar kulle a Kano na mako biyu biyo bayan ƙarewar wa'adin dokar a yau Litinin.
Boss Mustapha, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnati, shi ne ya sanar da hakan a wurin taron manema labarai na kullum kan matakan daƙile cutar korona ayau Litinin a Abuja.
Kazalika su ma matakan nesa-nesa da juna da aka É—auka da suka haÉ—a da zirga-zirga tsakanin jihohi an tsawaita su na mako biyu.
Rahoton da ta bayar a daren Lahadi, ma'aikatar lafiya ta Kano ta ce mutune 64 ne suka harbu da cutar a cikin sa'a 24 da suka wuce, yayin da aka sallami 18 sannan É—aya ya rasu.
Matakin tsawaita dokar na zuwa ne yayin da ake sa ran yin bikin Ƙaramar Sallah ranar Asabar ko Lahadi sakamakon gama azumin Ramadana.
Tuni makwabciyar Kano wato Kaduna ta sauya Asabar a matsayin ranar sassaucin dokar kullen , abin da ke nufin babu fita ranar idi.
Yanzu haka mazauna birnin Kano na iya fita domin siyayyar kayan abinci a ranakun Litinin da Alhamis, abin da ke nufin indai za a bar mutane su je sallar idi to sai an sauya ranakun sassauncin.
Duk da sassaucin fita na kwana biyu da mutanen Kano ke da shi, haramcin taruka da suka haÉ—a da na addini na nan daram.
Sai dai jihohin Borno da Adamawa da Gombe da Jigawa sun sassauta dokar kuma mazauna yankunan sun je masallatan Juma'a da majami'u tun daga ranar Juma'a.
Wannan ne mako na huÉ—u da jihar ta Kano ta kasance a kulle, sakamakon annobar korona.
Adadin masu cutar korona da aka samu a Kano ya kai 825, inda jihar ke biye wa Jihar Legas wadda ke da kusan kaso É—aya cikin uku na yawan masu cutar a Najeriya.
No comments:
Post a Comment