Buhari ya bai wa gwamnoni damar buɗe kasuwanni da masallatai da coci
Kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona a Najeriya ya ce za a buɗe dukkanin kasuwanni a Najeriya, yayin da wa'adin farko na mako biyu na sassauta dokar kulle ke cika a yau Litinin.
Sai dai Dr. Sani Aliyu, babban jami'i a kwamitin, ya ce gwamnoni ne za su tsara yadda za a buɗe kasuwannin.
Kwamitin ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai da jami'ansa ke gudanarwa yanzu haka a Abuja.
Sauran batutuwan sune:
Dokar bude jihohin zata fara yau da misalin karfe 10:00pm
Jirage za su ci gaba da zirga-zirga a tsakanin jihohi daga 21 ga watan Yuni
Haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi yana nan har sai an sake ji daga gare su.
Dokar hana fita - dake aiki a Abuja da Legas da Ogun - za ta koma daga 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe.
Makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe.
Otel-otel za su cigaba da harkokin su

No comments:
Post a Comment