ALAMOMI 10 NA WANDA DUNIYA TA AURA - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, August 15, 2020

ALAMOMI 10 NA WANDA DUNIYA TA AURA

ALAMOMI 10 NA WANDA DUNIYA TA AURA

1. Idan ya zamto Mutum ba ya jiran sallah saidai sallah ta jira shi.

2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur'anin ka ba (wai bakada lokaci).

3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka saÉ“awa ubangijinka.

4. Idan ya zamto kullum tunaninka yadda za kayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi.

5. Idan ya zamto baka karbar nasiha.

6. Idan ya zamto babu rayuwar da take
birgeka sai rayuwar mawaka da 'yan kwallo da makaÉ—a.

7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa'azi ko karatun al-qur'ani.

8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheria sai watarana.

9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin addininka sai dai na neman duniya (boko).

10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon bai Qareka da komai ba. 

Allah (swt) Ya yafe mana zunuban mu manya da qanana. Amin

No comments:

Post a Comment